✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya faru da Buhari kwana ɗaya kafin rasuwarsa — Mamman Daura

Mun yi hira sosai da shi har da dariya kuma yana sa ran za a sallame shi ya dawo gida a wannan makon.

Alhaji Mamman Daura, ɗan uwan marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana ganawa ta ƙarshe da ya yi da tsohon shugaban ƙasar gabanin ƙarewar kwanakinsa a duniya.

A wata hirarsa da Jaridar This Day, Mamman Daura ya ce yana tare da Buhari a ranar Asabar da ta gabata kuma har an fara shirye-shiryen dawowarsa gida Nijeriya.

“Mun yi hira sosai da shi kan abubuwa da dama har da dariya kuma yana sa ran za a sallame shi ya dawo gida [Nijeriya] a wannan makon.”

A cewar Mamman Daura, marigayin ya buƙaci a tabbatar da biyan kuɗin masaukin duk waɗanda suka je duba shi yayin da yake jinya a Landan saboda har an soma batun sallamarsa daga asibiti.

Mamman Daura ya ce ya bar Buhari wanda ya soma murmurewa a asibitin da yake jinya da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar Asabar, da zummar dawowa washegari da safiyar Lahadi saboda likita zai sake bincikar lafiyarsa a wannan rana.

“Na baro shi da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Asabar. Yana cikin ƙoshin lafiya da tsammanin zai ga likitansa da safiyar ranar Lahadi.

“Sai dai zuwa tsakar ranar Lahadi, rashin lafiyar tsohon shugaban ƙasar ta ƙara tsananta, inda numfashinsa ya riƙa ɗaukewa, kuma duk da ƙoƙarin likitoci na ceto ransa, zuwa ƙarfe 4:30 na yammaci wa’adinsa ya cika.”

Aminiya ta ruwaito cewa, tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya riga mu gidan gaskiya a ranar Lahadin da gabata, inda a wannan Talatar za a yi jana’izarsa a garin Daura da ke Jihar Katsina.