Tawagar jami’an tsaron haɗin gwiwa ta musamman da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya kafa domin yaƙi da ayyukan ’yan daba da sace-sacen waya a jihar, ta samu nasarar ƙwato makamai tare da cafke mutane 398 da ake zargi a wurare daban-daban.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda (PPRO), DSP Hassan Mansir ne ya fitar, na bayyana cewa, an kai samamen ne cikin gaggawa tare da wasu sahihan bayanan sirri.
- Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa Ibom
- Yin sulhu da ’yan bindiga dabara ce ba gazawa ba — Gwamnatin Sakkwato
Samamen ya sanya wasu da dama daga cikin masu aikata laifuka tserewa daga Jihar Kaduna saboda fargabar kama su.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, a cikin kwanaki tara na farko da rundunar take gudanar ayyukanta, ta kama wani mutum mai suna Mathew Adamu, wanda ya shahara wajen aikata ta’addancin cikin al’umma.
Sanarwar ta ce, rundunar ta ƙunshi rundunar ’yan sandan Najeriya ne a matsayin hukumar da ke jagorantar hukumar, tare da sojoji da Jami’an tsaron farin kaya DSS da Sibil defens da jami’an shige da fice na Najeriya da hukumar gyaran hali da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) da hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da Hukumar Kwastam ta Najeriya, ciki har da hukumar ’yan banga ta Jihar Kaduna (KADVIS).
DSP Hassan ya bayyana cewa, an samu wata ƙaramar bindiga ƙirar gida daga hannun wani mutum mai suna Adamu Umar, wani fitaccen mai sayar da miyagun ƙwayoyi, wanda za a miƙa ƙararsa ga Hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi.