✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai zarce Dubai daga India

A watan Oktobar bara aka dakatar da bai wa ’yan Najeriya bizar Dubai.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai garzaya birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), bayan kammala ziyarar aiki a Indiya.

A wannan Lahadin ce aka kammala taron G-20 na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya wanda Firaiministan India, Modi Norendri ya kasance mai masaukin baki a birnin New Delhi.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Cif Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Tinubu zai yada zango a Hadaddiyar Daular Larabawan domin karasa warware matsalar hana ’yan Najeriya bizar zuwa Dubai da mahukunta kasar suka yi.

A cewar Ngelale, “Tinubu zai soma yada zango a Hadaddiyar Daular Larabawa bayan ziyarar aiki da ya yi a birnin New Delhi na India.

“Tinubu zai yi amfani da wannan dama domin ci gaba da tattaunawa wajen warware wasu muhimman batutuwa da suka danganci alakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da UAE.”

Ana iya tuna cewa, a watan Agustan da ya gabata ne Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta warware sabanin da ke tsakanin Najeriya da kamfanin jiragen sama na Emirates EMIRA.UL da kuma bayar da bizar zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.

Aminiya ta ruwaito cewa Daular Larabawa ta dakatar da bayar da biza ga ’yan Najeriya ne a shekarar da ta gabata, bayan da kamfanin jirage na Emirates ya dakatar da zirga-zirgarsa zuwa kasar saboda gazawar samun kudadensu da suka makale a Najeriyar wacce ta fi kowace kasa girman tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Dangane da hakan ne ma tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a dambarwar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda ta kai ga kasar ta Gabas ta Tsakiya ta dakatar da bai wa ’yan Najeriya takardar izinin shiga cikinta, wato biza.

A watan Oktobar bara ne hukumomin Daular suka dauki matakin dakatar da bai wa ’yan Najeriya bizar, sai wadanda suke da fasfo na manya wato na diflomasiyya kawai.

Duk da cewa hukumomin kasar ta Larabawa ba su bayyana dalilinsu na daukar matakin ba, wasu na danganta shi ga rashin da’a da bin doka da oda da wasu ’yan Najeriyar da ke zaune ko aiki a can suke yi.