✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na sane ya naɗa ‘yan Arewa a manyan muƙamai- Ribaɗu

Tinubu ba mu dama. Saboda haka a yanzu ya rage mana mu ’yan Arewa mu yi abin da ya kamata.

Mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribaɗu, ya ce Shugaba Tinubu yana sane ya naɗa ‘yan arewa manyan muƙaman ƙasar nan.

Ribaɗu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin gabatar da jawabai a shirye-shiryen bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Usman Ɗanfodio da ke Sakkwato .

Ribadu ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya miƙa wa ’yan Arewa ragamar jagorancin wasu manyan muƙamai masu muhimmanci saboda yana son a kawo ƙarshen matsalar da take addabar yankin.

A yayin gabatar da maƙala kan “shawo kan matsalolin tsaro da yankin Arewa ke fuskanta a Najeriya”, ya nuna rashin jin daɗinsa kan matsalolin da Arewa ke fuskanta kama daga ƙalubalen tsaro zuwa yaran da ba sa zuwa makaranta da dai sauransu .

Ya kuma ƙara da cewa talaucin da yankin ke ciki na ƙara ta’azzara a kullum.

“Yayin da Tinubu yake gudanar gwamnatinsa, ya sanya Arewa a tsakiyar zuciyarsa kuma yana shirin yin komai domin ceto yankin daga halin da yake ciki.

“Wannan ne ya sa ya naɗa ‘yan Arewa a manyan muƙamai. Ya miƙa wa Arewa  tsaro da ma’aikatar tsaro. Ya ba mu ministocin noma da ilimi. Ya kuma ba mu Ministan Lafiya da Harkokin Waje a yunƙurinsa na juya dukiyoyin yankin.

“Ya [Tinubu] ba mu dama. Yanzu saura na kanmu mu ’yan Arewa. Mu ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninmu a gefe, mu yi aiki don ci gaban yankinmu da Najeriya,” inji shi.

Dangane da rashin tsaro kuwa, ya ce gwamnati mai ci ta samu nasarori da dama, inda ya ba da misali da wasu kwamandojin ‘yan bindiga da jami’an tsaro suka kashe a baya-bayan nan, tare da kuɓutar da dubban waɗanda aka sace ba tare da biyan ko sisin kwabo ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, Ribadu ya yi jawaban ne a yayin da aka soma shirye-shiryen bikin yaye ɗaliban aji na 38, 39, 40 da kuma 41 na Jami’ar Danfodiyo da ke birnin na Shehu.