Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar.
Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma, a cewar ma’aikatar tsaron jihar.
Kwamishinan tsaron jihar, Nasir Mua’zu ya sanar da haka ne a martaninsa kan wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta, waɗanda ya ce ana amfani da su domin tayar da hankalin jama’a.
Mu’azu ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana yin iya bakin koƙarinsa wajen shawo kan matsalar ’yan ta’adda kuma ana samun nasara a kansu.
Kwamishinan ya ce lokacin da Gwamna Raɗɗa ya karbi shugabancin Jihar Katsina, ƙananan hukumomi aƙalla 24 ne ke fama da matsalar ’yan bindiga, amma kuma sakamakon haɗin kai da jami’an tsaro da kuma ƙirƙiro ƙungiyar ’yan sa-kai ta jihar, an yi nasarar murƙushe su a ƙananan hukumomi 11.
Mu’azu ya ce, matsalar ta kuma yi sauƙi a wasu ƙananan hukumomi tara, in banda Faskari da Ƙankara da Safana da kuma Matazu, da ke ci gaba da dama da hare-hare.
Ya bayyana cewa hakan ba ya nufin cewa gwamnati ta gaza, domin jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaron lafiya da duniyoyin al’umma a wuraren.
A cewarsa, duk da hatsarin da gwamnan ya yi kwanakin baya, bai daina tattaunawa da shugabannin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ba da ke jihar, domin shawo kan matsalar.
Don haka ya buƙaci haɗin kai daga kowanne ɓangare, musamman ganin yadda jami’an tsaron ke sadaukar da rayukansu wajen kare lafiya.