Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya bayyana ƙwarin guiwar cewa darajar Naira a kasuwar hada-hadar hannayen jari za ta ci gaba da samun tagomashi ta fuskar daraja yayin da Dala ke ci gaba da faɗuwa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce, dole ne Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen tallafin man fetur sannan kuma ya tabbatar da haɗewar kuɗaɗen musaya da yawa saboda “tsohon tsarin yana samar da hamshaƙan attajirai dare ɗaya.”
- EFCC za ta iya kama Yahaya Bello idan ta so – Bwala
- Rashin Tsaro: Nijeriya na kunyata duniya — T.Y Danjuma
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da ayarin ƙungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Gabriel Idahosa ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke fadar shugaban ƙasa Villa a Abuja.
Ya ci gaba da cewa, a lokacin da Naira ta daina samun tagomashi, wasu suna ta murna, “amma a ciki muna yi musu dariya saboda mun san cewa muna da shugabancin da za mu bi don sauya yanayin.
“Asiwaju ya san tsarin, kuma a gaskiya Naira na samun karɓuwa kuma tazarar da ke tsakanin darajarta da Dalar Amurka za ta ƙara raguwa.”
Sanata Shettima ya tunatar da cewa, “irin jagorancin da shugaba Tinubu ya samar a lokacin da yake Gwamnan Legas ne ya kafa harsashin ci gaban da aka samu a jihar har kawo yanzu.
“Saboda haka za mu ci gaba gode wa shugaban ƙasa Tinubu da ya kawo makamancin tsarin ci gaban Legas da muke gani yau.”
Shettima ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin Tinubu na yin iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta magance ƙalubalen da ake fuskanta a fannin wutar lantarki domin ta san cewa wutar lantarki na da matuƙar muhimmanci.
“Mun kuduri aniyar ganin mun samar da ayyukan yi ga matasanmu.
“Maganar gaskiya, fatan Shugaban ƙasa shi ne mu ɗaukaka ta hanyar kai ƙasar nan zuwa ga tudun mun tsira.
“Yana son barin abin da za a gada, na shugabanci nagari, da fatan ƙasashen nahiyar Afirka za su koyi da Najeriya.
“Ina so na tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fahimci duk wata matsala da yanayin da muke fuskanta, saboda haka a wannan gwamnatin, kuna da aboki makusanci,” in ji Shettima.