Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa Jihar Katsina domin ziyarar aiki ta kwana biyu, inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi.
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda, da tsohon Gwamna jihar Bello Masari na cikin manyan mutanen da suka tarɓe shi tun daga filin jirgin Umaru Musa.
- Tinubu zai yi shekara takwas yana mulki – Afenifere
- Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya
Bayan isarsa ne kuma ya yi wa rundunar sojin ƙasar jawabi.