Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta biya wa maniyyatan jihar 2,047 kuɗin hadaya domin sauƙaƙa musu wajen hidimomin aikin Hajji na shekarar 2025.
Amirul Hajji kuma Mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake yi wa mahajjatan jirgin farko bankwana kafin tashin zuwa ƙasa mai tsarki.
- An tafka asara bayan gobara ta ƙone Kwalejin Sheikh Dahiru Bauchi
- Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa
Ya ce an biya wa kowane maniyyaci Riyal 600.
Mahajjatan da za su fara tafiya sun fito ne daga ƙananan hukumomin kudancin jihar, kuma za su tashi a jirgin kamfanin Max Air.
Gwamna Radda ya ja hankalin maniyyata da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin aikin Hajji.
Haka kuma ya roƙe su da su yi addu’a don samun zaman lafiya da ci gaban Jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.
A shekarar da ta gabata ma, Gwamna Radda ya biya wa mahajjatan jihar kuɗin hadaya domin rage musu kashe kuɗi a aikin Hajji.