✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya

An gano kayayyakin da aka sace, kuma an miƙa su ga rundunar ’yan sandan Najeriya inda ta fara gudanar da cikakken bincike.

Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya, NRC ta tabbatar da kama ma’aikacinta mai suna Gift Eseeli, mai shekara 38, bisa zargin satar waya a Rafa Yard da ke kan hanyar Warri-Itakpe a harabar tashar jirgin ƙasa (WITS) Jihar Delta.

Jami’an rundunar Man O’war na shiyyar Railway Command ne suka kama ma’aikacin.

A cewar mai magana da yawun hukumar ta NRC, Callistus Unyimadu, binciken farko na nuni da cewa an cire dogayen wayoyin da suke ba da sigina masu sulke mai tsayin 50mm daga na’urorin gefen titin kafin jami’an ‘yan banga ƙarƙashin jagorancin Mista williams Agiake su cafke wanda ake zargin.

An gano kayayyakin da aka sace, kuma an miƙa su ga rundunar ’yan sandan Najeriya inda ta fara gudanar da cikakken bincike.

Manajan Darakta na NRC Dakta kayode Opeifa, a cikin sanarwar ya yi Allah wadai da faruwar lamarin tare da jaddada cewa waɗanda aka samu da laifin lalata dukiyar ƙasa za su fuskanci fushin doka.

“Kadarorin titin jirgin ƙasa mallakin kadarorin ƙasar Najeriya ne. Ayyukan ɓarna na barazana ga lafiyar fasinjoji tare da yin zagon ƙasa ga ayyukan muradun sabuwar Najeriya na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”

Ya ce, Hukumar ta NRC za ta gurfanar da duk wani mutum ko ƙungiya ciki har da ma’aikatan da aka samu da laifin yin ɓarna ba tare da ƙetare iyaka ba.