Ana fargabar cewa wata sabuwar amarya mai suna Amina Abashe, ta antaya wa angonta ruwan zafi sakamakon sabanin da suka samu sanadiyyar yawan waya da take yi da wasu mazajen.
Angon mai suna Shehu Abdullahi wanda ya zanta da Aminiya ta wayar tarho daga gadon asibitin da yake jinya a Karamar Hukumar Kontagora ta Jihar Neja, ya ce ya auri amaryar tasa watanni biyu da suka gabata bayan rasuwar tsohuwar matarsa.
- Ƙunci ya sa ’yan Arewa buɗa-baki da ruwa zalla a Kalaba
- Marigayi Olubadan Lekan ya kafa tarihi— Sarkin Yarbawan Kano
Angon wanda yake jinya a Babban Asibitin Kontagora, ya ce da farko dai amaryar ransa ta nema bayan ta yi yunkurin daba masa wuka.
Ya ce, sai dai bayan hakarta ba ta cimma ruwa ba sakamakon kwace wukar da ya yi daga hannunta, sai ta debo tafasasshen ruwa ta antaya masa a jikinsa.
Abdullahi ya yi bayanin cewa tun bayan auren ne suka soma samun matsala da amaryar wadda ta hau kujera naki kan tarewa a gidansa har sai da ya kai korafi gidan iyayenta.
Ya ce, a Yammacin Talatar da ta gabata ranar da lamarin ya auku, ta kira shi a waya tana son ganinsa a gidansu, inda bayan ya hallara ta shaida masa cewa ta gaji da auren kuma tana da wani saurayin wanda zai mayar masa da sadakin da biya na aurenta.
Ya ce, a daidai wannan lokaci da ta shaida masa hakan ne kuma ta ci gaba da waya da mutumin wanda yana zargin shi ne saurayin da ta yi masa bayani a kai.
Ya kara da cewa, “cikin fushi na yi kokarin kwace wayar da hannunta amma ta dauko wuka za ta daba min amma na samu sa’ar kwacewa daga hannunta.’’
Kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya ci tura.