’Yan bindiga sun kashe wata mata da suka sace tare da mijinta Yakubu Dada watanni bakwai da suka gabata a yankin Kontagora da ke Jihar Neja.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan sun halaka matar mai suna Lami bayan karɓar Naira miliyan 10 kuɗin fansa.
Kazalika, ’yan bindigar sun kuma nemi ƙarin Naira miliyan 20 da baburan Bajaj huɗu, tare da yin barazanar kashe mijinta muddin aka gaza kai musu abubuwan da suka buƙata.
Aminiya ta ruwaito cewa, tun a ranar 31 ga watan Oktoba na 2024 ne Yakubu Dada da mai ɗakinsa suka faɗa tarkon masu garkuwa yayin da suke kan hanyar zuwa Kontagora.
Da take zantawa da wakilinmu, uwargidan magidancin mai suna Maimuna, ta ce sun cefanar da kusan duk abin da suka mallaka ciki har da gidaje, motoci, gadaje, akwatin talabijin domin tara kuɗin fansar naira miliyan 10 da suka biya a watan Nuwamban bara.
Ta ce wani ƙanin mijinsu ne ya kai wa masu garkuwar kuɗin fansar a wani daji a Jihar Kebbi, amma daga bisani suka nemi ƙarin naira miliyan 60 sannan suka sassauta zuwa naira miliyan 20 da har kawo yanzu sun gaza biya.
Maimuna wadda ta ce masu garkuwa sun kashe abokiyar zamanta a ranar Lahadin da ta gabata, ta buƙaci gwamnatin jihar Neja da hukumomin tsaro da su shiga lamarin domin ceto mijin nasu.
Wani makwabci, Idris Mohammed, ya ce an yi kiran neman tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa a yayin sallar Juma’ar da ta gabata tun kafin labarin mutuwar Lami.
Aminiya ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, sai dai ya yi alƙawarin zai bibiyi lamarin gabanin cewa komai a kai.