Jami’an hukumar tsaro ta DSS da na rundunar sojojin Najeriya sun ce sun hallaka ’yan bindiga akalla 45 a kusa da garin Kuchi da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.
An dai sami nasarar ce sakamakon wani harin da dakarun suka kai cikin sirri a ci gaba da yakin da suke yi da ’yan bindiga a yankin.
Majiyoyi daga cikin jami’an tsaro sun bayyana cewa jami’an DSS sun bi sahun wasu ’yan bindiga ne inda suka dakile yunkurinsu na kai munanan hare-hare, wanda kasurgumin dan bindigar nan, Dogo Gide da yaransa suka shirya kai wa.
Majiyar ta ce bayanan sirrin da hukumar ta tattara sun nuna yadda ’yan bindigar wadanda suka yi sansani a dajin Bilbis da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara da ma wasu sassan jihar Kaduna, Dogo Giden ne ya gayyace su domin su kai hari yankin na Kuchi.
A cewar amjiyar, “Da sanyin safiyar Litinin, biyu ga watan Yunin 2025, ’yan bindiga wajen su 100 daga kauyukan Kaduna da Zamfara da ke dauke da muggan makamai suka tunkari garin Kuchi na karamar hukumar Munya a jihar Neja.
“To sai dai jami’an tsaro sun yi musu kwanton bauna a wajen garin na Kuchi. Lamarin dai ya kai ga musayar wuta, inda aka kasha da dama daga cikin maharan sannan aka raunata wasu, aka kwace Babura da makamansu. Sai dai rahotanni sun nuna cewa wasu jami’an DSS su biyar sun ji rauni kuma yanzu haka suna asibiti.”
Majiyar ta ce harin wanda ya biyo bayan wani kisa da aka yi wa ’yan bindigar su 50 ya yi wa Dogo Giden mummunar barna.