Akalla mutane hudu ne, ciki har da wani matashi dan shekara 13, aka ce an harbe su tare da fille kawunansu a ranar Alhamis a yankin Gangaran Kwata da ke karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Mazauna yankin sun ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe biyu na tsakar daren ya haifar da tashin hankali a yankin na Mangu.
- Sojoji sun dakile hare-haren ‘Yan Boko Haram biyu a Borno
- Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
Abdullahi Maicibi, shugaban addini a yankin Kwata, ya tabbatarwa da wakilin Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce an dauki gawarwakin wadanda aka kashe zuwa babban masallacin Mangu da ke garin Mangu domin yin sallar jana’iza.
Shagari Madaki, another resident, said apart from the murders, many houses were burned during the incident, explaining that “We don’t know why the attackers invaded our area,” he added.
Wani mazaunin garin Shagari Madaki ya ce baya ga kashe-kashen da aka yi, an kona gidaje da dama a lokacin da lamarin ya faru, yana mai bayanin cewa “ba mu san dalilin da ya sa maharan suka mamaye yankinmu ba.”
A cewar shugaban addinin, wasu mutane dauke da makamai da ake zargin ‘yan kungiyar Mwaghavul ne suka mamaye yankin, inda suka yi ta harbe-harbe inda kashe mutum hudu.
Malamin addinin ya jaddada bukatar jami’an tsaro su dauki kwakkwaran mataki domin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika, yana mai cewa barin wadanda ba gwamnati ba su dauki makami a kan daidaikun mutane zai haifar da rashin bin doka.
Musa Ibrahim, kawun daya daga cikin mamatan, ya bayyana cewa suna tare da dan uwansa ne a lokacin da suka ji karar harbe-harbe.