✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan sun sha ‘Kayan Mata’

Kishiyoyin biyu da ke yankin Dakwa a Abuja sun sha maganin gargajiyan, wanda aka fi sani da kayan mata ne, kwana uku bayan amaryar da…

An kwantar da wasu matan aure kishiyoyin juna a asibiti bayan da suka sha maganin kara sha’awa domin burge mijinsu bayan ya auro mata ta uku.

Kishiyoyin biyu da ke yankin Dakwa a Abuja sun sha maganin gargajiyan, wanda aka fi sani da kayan mata ne, kwana uku bayan amaryar da mijinsu ya auro ta tare.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, mijin nasu ya ce bayan kai su asibiti ne aka yi musu gwaji aka gano cewa wasu gaɓoɓinsu sun samu matsala, wanda ake zargin maganin da suka sha ne ya haddasa.

Ya ce, “ina gidan amarya aka kira ni cewa matana ba su da lafiya, inda na je na samu suna birgima cewa cikinsu na ciwo. Sai na kira wata nas ta duba su ta su magani ta yi musu ƙarin ruwa amma basu sani ba.

“Shi ne sai da muka kai su asibitin Madallah da ke Jihar Neja.

“A nan ne aka yi musu gwaji aka gano cewa wasu gaɓoɓinsu sun samu matsala, aka yi musu aiki,” in ji shi.

Magidancin mai suna Musa Muhammad ya bayyana cewa sallamo matan nasa a ranar Litinin, kuma an gano cewa sun sayi kayan matan ne a wajen wata wata mai tallar maganin gargajiya da suka saba saya.

Magidancin wanda ya ce yana ƙoƙarin gano matar domin kare wasu mata daga faɗawa a tarkonta, ya bayyana cewa matan nasa sun saba maganin na ruwa a wurin matar wanda suke haɗawa da madara, amma a wannan karon sai ta canza ta ba su na gari.

Shan kayan mata na daga cikin abubuwan da suka zama ruwan dare a tsakanin mata, inda masana kiwon lafiya ke gargaɗi game da haɗarinsi ga lafiyarsu da matucinsu.