Wani matashi mai shekaru 30 ya kashe kansa bisa rahotanni bayan rasuwar ƙaramar matarsa a ƙauyen Ikumi da ke Ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja.
Majiyoyi sun bayyana cewa magidancin mai mata biyu ya sha fama da matsalolin tunani da na zuciya tun bayan rasuwar matarsa ta biyu a watan Maris na wannan shekara.
Sun ƙara cewa ya kasance yana yawan bayyana cewa ba zai iya samun kwanciyar hankali ba tare da marigayiyar ba.
Shaidu sun bayyana cewa ya yi amfani da bindigarsa ta toka wacce yake farauta da ita wajen harbe kansa har lahira a gonarsa.
Wata majiya ta ce ya bar matarshi ta farko da manya da kuma yara biyu. Kakakin ’yan sanda a Jihar Nijar, SP Wasiu Abiodun, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 24 ga Afrilu, 2025.
- ’Yan kasuwar da suka ɓoye kayan abinci na tafka asara
- Na shiga fim ne don isar da saƙon Musulunci — Malam Inuwa Ilyasu
- ’Yar Arewa da ta kafa tarihin samun Digiri Mai Daraja ta ɗaya a fannin Shari’a
A cewarsa, “A ranar 24 ga Afrilu, 2025 da misalin ƙarfe 8 na dare, an samu rahoto cewa wani Stephen Moses mai shekaru 30 daga ƙauyen Ikumi ta yankin Shako na ƙaramar hukumar Gawu-Babangida, ya harbe kansa a kirji da bindiga a gonarsa da rana.
“Jami’an ’yan sanda na Gawu-Babangida sun ziyarci wurin da abin ya faru, sun samu bindiga da kuma gawar a ƙasa, an kai gawar asibiti yayin da bincike na farko ya nuna cewa mamacin yana cikin zaman makokin rasuwar matarsa wacce ta rasu kwanan nan, kuma ya kasance yana barazanar kashe kansa, amma ’yan uwansa ba su sanar da ’yan sanda ba don ɗaukar matakan kariya.”