✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwar kasko: Mai gida da dan fashi sun kashe juna a Abuja

Magidancin ya gamu da ajalinsa ne bayan bata-garin sun caka masa wuka a yankin Tsohuwar Kutunku da ke Karamar Hukumar Gwagwalada.

Wani magidanci ya yi mutuwar kasko da wani mai sana’ar jari-bola, bayan da gungun wasu ’yan jari-bola suka yi kokarin cire tagar gidansa da karfin tsiya a yankin Babban Birnin Tarayya.

Magidancin, wanda ke sana’ar sayar da tufafin gwanjo ya gamu da ajalinsa ne bayan bata-garin sun caka masa wuka a yankin Tsohuwar Kutunku da ke Karamar Hukumar Gwagwalada.

Wani dan unguwar mai suna Francis Nnamdi, ya ce da misalin karfe 9.26 na dare ne wasu mutum uku masu sana’ar bola-jari suka je gidan mutumin, suna kokarin cire karfen tagarsa.

Ya ce cewa bayan mai gidan ya gan su ne ya tunkare su domin jin dalilinsu na neman cire masa tagogi, inda a garin haka daya daga cikinsu ya zaro wuka.

Ganin haka ne mutumin ya shiga daki ya dauko adda, kuma a garin rikicin masu bola-jarin suka caka masa wuka, shi kuma ya mayar da martani ta hanyar saran dayansu da addar hannunsa, ragowar kuma suka tsere, suka bar dayan kwance a cikin jini.

Ya ce daga bisani makwabta suka kira ’yan sanda, suka dauke gawarwakin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, inda likitoci suka sanar cewa dukkansu sun mutu, aka ajiye gawarwakin a mutuware.

Mun nemi karin bayani daga kakakin ’yan sanda na Babban Birnin Tarayya, SP Adeh Josephine, amma ta shaida wa wakilinmu cewa ba ta samu rahoton lamarin ba, amma za ta bincika.