Mazauna Babban Birnin Tarayya za su fuskanci katsewar ruwan sha na tsawon makonni biyu, kamar yadda Hukumar Kula da Ruwa ta yankin ta sanar.
Rashin ruwan, wanda ya fara ranar Juma’a, 30 ga Mayu, ana sa ran za ta ci gaba har zuwa ranar Juma’a, 13 ga Yuni.
Matsalar ta samo asali ne daga ayyukan gyare-gyare da ake yi a tashoshin tace ruwa na madatsar ruwa ta Lower Usuma Dam.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, gyare-gyaren sun shafi muhimmin aikin haɗa kayan aikin lantarki da injiniya, wanda babban bangare ne na aikin inganta matatar.
- Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba
- Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno
Wannan aiki ya tilasta dakatar da rarraba ruwa na ɗan lokaci zuwa tsakiyar birnin da kuma yankunan wajenta.
Hukumar ta shawarci jama’a da su tanadi isasshen ruwa da zai ishe su tsawon lokacin, sa’annan su nemi wasu hanyoyin samun ruwa don biyan bukatunsu.