✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FCTA ta rufe hedikwatar PDP saboda rashin biyan haraji

Hukumar ta ce daga yau Litinin za ta ci gaba da ƙwace kadarorin da suka shafe shekaru ba su biya haraji ba.

Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA), ta rufe hedikwatar jam’iyyar PDP da ke unguwar Wuse a Abuja.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:05 na ranar Litinin.

Jami’an FCTA sun isa ginin tare da jami’an tsaro, inda suka rufe ofishin.

Wasu ma’aikata sun nuna rashin jin daɗinsu, bayan tafka sa-in-sa na tsawo mintuna 15, jami’an FCTA sun bar ma’aikata su fitar da motoci da kayayyakinsu kafin kulle ginin.

A makon da ya gabata, FCTA ta sanar da cewa za ta ƙwace sama da kadarori 4,700 a Abuja saboda rashin biyan haraji na tsawon shekaru 10 zuwa 43.

Waɗannan kadarorin suna yankunan Central Area, Garki, Wuse, Asokoro, Maitama da Guzape.

FCTA, ta ce mallakar waɗannan filaye ya koma hannun gwamnati.

Tun daga Litinin, gwamnati ta fara ƙwace su ba tare da la’akari da wanda ya mallaki kadarar ba.

Daraktan Sashen Kula da Ci Gaban Birnin Tarayya, ya ce za a rufe waɗannan gine-gine kuma ba za a bari kowa ya shiga ba.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta yanke hukunci kan yadda za a yi da su a nan gaba.

Daraktan Sashen Filaye, ya bayyana cewa babu wani hukuncin kotu da ya hana FCTA ɗaukar matakin da ta ke ɗauka a yanzu, don haka za su ci gaba da yin aikinsu.

Ya kuma ce suna tantance kadarorin da suka daɗe ba su biya haraji ba daga shekara ɗaya zuwa 10, kuma za su ɗauki mataki bayan sun kammala tantancewar.

Tun a watan Maris, 2025 FCTA, ta sanar da soke takardun mallakar filaye guda 4,794 saboda rashin biyan haraji, inda ta gargaɗi cewa za ta fara karɓe ikon mallakar filayen daga ranar Litinin.