✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wike ya rufe ofishin FIRS da Bankin Access kan rashin biyan haraji

Ana bin ginin da bankin Access yake bashin harajin shekara 35, ofishin FIRS kuma bashin harajin shekara 25.

Hukumar Kula da Babban Birnin (FCTA) Tarayya ta rufe ofishin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kuma ginin Bankin Access kan rashin biyan haraji na sama da shekaru 25.

Daraktan Kula da Filaye na Hukumar FCTA, Chijioke Nwankwoeze, ya bayyana cewa hukumar bin ginin da bankin Access yake bashin harajin shekara 35, ofishin FIRS da ke unguwar Wuse Zone 5 kuma bashin harajin shekara 25.

Babban Ofishin na FIRS na daga cikin fitattun gine-gine da Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji na Babban Birnin ta rufe a safiyar Litinin, kan zargin rashin biyan haraji.

Sauran sun  shafa da ginin Bankin Access da da ofishin kamfanin mai Total Energy da fitaccen otel din Ibro Hotel a unguwar Wuse, da sauran wurare 4,700 a Abuja.

Chijioke Nwankwoeze, ya bayyana cewa ginin bankin Access da matakin ya shafa, mallakin wani wani kamfani ne, inda bankin ta kama haya.

Kazalika hukumar ta kwace izinin mallakar wasu filaye a wasu fitattun unguwanni saboda matsalar rashin biyar harajin.

Daraktan Kula da Bunƙasa Birnin Abuja, Mukhtar Galadima, ya jagoranci aikin ne bayan hukumar ta fitar da sanarwar rashin biyan harajin da ya kamata.

Ya bayyana cewa ana bin kamfanin Total harajin Shekara 10, wanda ya cika a watan Maris na 2025.

Fili mai lamba 2456 da ke titin Cadastral Zone A02, a unguwar Maitama, mallakin Kamfanin Rana Taher Furniture saboda rashin biyan harajin kas ana shekara 34.

Galadima ya bayyana cewa aikin zai ci gaba a sauran unguwannin Abuja, yana mai gargaɗin waɗanda abin ya shafa su gaggauta yin abin da aya kamata, ko su kuka da kansu.

Hukumar FCDA ta tsaurara matakan karbar haraji, musamman kam dokokin da suka shafi gine-gine da mallakar kasa a ƙarƙashin Minista mai ci, Barista Nyesom Wike.

Ya bayyana cewa wajibi ne masu filayen da hukumar ta kwace su tashi nan take, su bi hanyar da ta dace domin warware duk wata matsala.