’Yan sanda sun tsare wata matar aure kan zargin ta da kashe kishiyarta a Ƙaramar Hukumar Daura da ke Jihar Katsina.
Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa matar ta yi wa uwargidarta kisan gilla ne bayan wata hatsaniya da aka samu a tsakaninsu, wanda ya ƙazance har ya kai ga kisa.
Amaryar, mai shekara 23 a duniya, ta yi wa uwargida wannan aika-aika ne ranar Lahadi a unguwar Sabon Gari, daura da Makaranta Firamare ta Daɗi.
DSP Abubakar Aliyu, ya ce a ranar ce bayan mijinsu ya dawo daga kasuwa ya kai ƙara Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Daura cewa ya iske uwar gidansa kwance a cikin jini.
- An yanke wa wanda ya yi wa agolarsa fyaɗe ɗaurin rai-da-rai
- Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano
- NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su
“Ya bayyana cewa an sossoka wa matar tasa wuƙa, lamarin da ya sa DPO ya jagoranci jami’ansa suka je aka kai ta Babban Asibitin Tarayya na Daura, inda likita ya bayyana musu cewa rai ya riga ya yi halinsa,” in ji DSP Abubakar Aliyu.
Ya bayyana cewa a yayin bincike, an kama kishiyar amaryar, kuma ta amsa cewa ita ce ta kashe uwargidar bayan sun ba hamata iska saboda wani saɓani da suka samu.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Katsina, Bello Shehu ya bayyana cewa za a gurfanar da wadda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.
Ya kuma buƙaci jama’a da su guji hawa dokin zuci ko ɗaukar doka a hannunsu.