Mahaifin angon da ’yan uwan angon na jini da danginsa na daga cikin mutane 13 da aka yi wa kisan gilla a hanyar ɗaurin auren ango, inda aka ƙona gawarwarkin wasunsu a cikin motar da ta ɗauko su, a yankin Mangun da ke ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Mahaifiyar angon, Malama Faji Sani da ke zaune a ƙauyen ɗan Bami Anguwar Rimi a ƙaramar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, ta shaida wa Aminiya cewa mijinta da ’ya’yanta biyu da ƙannenta biyu da kuma kishiyarta, na cikin mutanen da aka kashe su a harin na ranar Juma’a da dare.
Ta ce mijin nata, Alhaji Sani, wanda da shi suka dogara, ya rasu ya bar ’ya’ya 13 da jikoki da dama. “Shi maigidana shi ne bangon da muka dogara da shi, ga shi kuma yanzu babu shi. Don haka nake roƙon gwamnati da ta taimaka ta biya mu diyyar waɗanda muka rasa don sauƙaƙa mana raɗaɗin da muke ciki, tare da ci gaba da ɗaukar nauyin sauran yaran da ya rasu ya bari,” in ji dattijuwar.
Malama Faji ta ƙara da cewa duk waɗanda aka kashen ’yan uwan juna ne daga tushe ɗaya, suka haɗu domin tafiya ɗaurin auren ɗan nata.
- Za a yi wa Aminu Ɗantata Salatul Ga’ib a Kano
- Za a tono gawar tsohon Gwamna Alao-Akala domin gwajin ƙwayoyin halitta
Ta bayyana matuƙar kaɗuwa da samun labarin lamarin, cewa, “Na kaɗu sosai, sai ina jin labarin kamar a mafarki, na kasa yarda cewa labarin tabbatacce ne.”
‘Ganawarmu ta ƙarshe’
Shi ma ɗan uwan angon, Haruna Idris, ya ce yana tsaye matafiyan suka bar ƙauyen, su 32 a cikin motar, mata biyar, sauran kuma maza.
Ya ce mahaifinsa da yayyensa biyu da ƙanensa sun rasu a iftila’in. Haruna wanda ya ce a ranar farko an sanar da su ta wayar tarho cewa mutum tara ne suka rasu, daga baya kuma aka ce sun kai 11, daga nan aka daina ba su su bayani don gudun a tayar musu da hankali.
Ya ce, “A matsayinmu na Musulmi mun ɗauki ƙaddara domin mun yarda mutuwa daga
Allah take zuwa,” sa’annan ya roƙi gwamnati da ta gaggauta biyan su diyya don ci gaba da kula da marayu da mata da mamatan suka bari.
Haruna ya kuma roƙi a dawo da manjiyatan daga Asibitin Koyarwa na Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya don ba wa ’yan uwansu damar kula da su yadda ya kamata.
Yadda bin ya faru
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, Ibrahim Umar, ya bayyana wa Aminiya daga gadon asibiti, inda yake samun kulawa, cewa, “Mun kusa kaiwa Qu’an Pan wajen ɗaurin auren ɗan uwanmu, shi ne muka yi ɓatan kai saboda ba mu san hanyar ba. Mun tsaya tambayar wasu mutane kwatance, kafin mu farga sun yi mana ƙawanya suna ihu cewa a kashe mu, wai mu Hausawa ne.
“A nan suka fara duka da kawo mana hari da makamai. Direbanmu suka fara kashewa kafin sauran mutanen, suka cinna wa motar wuta da gawarwakin a ciki.”
Ibrahim Umar, wanda ya ce angon ɗan yankin Zariya ne da ke koyarwa wata babbar cibiya a yankin, ya bayyana cewa, “An kashe mahaifin angon da kawunsa da ƙaninsa. Mun yi ƙoƙarin yi wa mutanen bayani cewa ɗaurin aure za mu je, ga goro da alawa da kayan ɗaurin auren, amma ba su saurare mu ba. A inda angon ke koyarwa ne ya haɗu da matar da zai aura, duk mun yi wa mutanen bayani, amma suka ƙi.”
Matashin ya ce, Allah ne Ya taimaka sojojin da ke sintiri a yankin suka kawo mana ɗauki, amma da abin ya fi haka muni.
Shi ma Sa’adu Abdullahi, wanda ya sha da ƙyar a harin, ya ce, “sun kashe yayyaina da ƙannena, sun ɗauke wayoyinsu.”
Wata mai suna Maimuna a cikin matafiyan, ta ce: “Muna waya da angon yana mana kwatance, har yake ce mana mu yi tambaya idan ba mu gane hanya ba. Mun tsaya yin haka sai mutanen garin suka yi mana dirar mikiya, kafin ƙiftawa da bismillah sun kewaye mu kowannensu ɗauke da makami”.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) da ke Mangu, Sheikh Suleiman Haruna, ya shaida wa wakilinmu cewa an ajiye gawarwakin a Babban Asibitin Mangu, inda daga bisani aka yi jana’izarsu, kuma “Shugaban ƙaramar Hukumar Mangu ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a kan lamarin.”
Malamin ya bayyan cewa mutum 13 ne suka mutu a lokacin, a yayin da wasu 18 suke asibiti. Ya ce an yi jana’izar mutum tara a ranar Asabar a Maƙabartar Unguwar Hayi, bisa izinin dangin matafiyan, domin gujewa tashin hankali idan aka kai gawarwarkin garinsu. Ragowar mutanen kuma a ƙaramar Hukumar Qu’an Pan aka binne su.
Malamin ya yi kira ga “gwanatin jiha da ta tarayya su ɗauki tsattsauran mataki da zai zama darasi ga masu wannan ɗabi’a da kuma kawo ƙarshen matsalar tare matafiya ana kashe su.
Wakilinmu ya lura cewa bayan aukuwar lamarin an girke sojoji da ’yan sanda a muhimman wurare a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, domin tabbatar da bin doka.
Aminiya ta ruwaito cewa an kai wa matafiyan hari ne da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar Juma’ar da taka gabata, a lokacin da ayarinsu ciki har a ƙananan yara, suke tafiya a cikin wata bas mallakin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya.
Sun fito ne daga yankin ƙaramar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, amma maharan suka tare su, suka kashe har da direban motar, wanda ma’aikacin jami’ar ABU ne.
A kamo maharan a hukunta su — Tinubu
Fadar Shugaban ƙasa, a saƙon ta’aziyyarta, ta sanar da umarnin Shugaba Bola Tinubu ga jami’an tsaro cewa su yi duk mai yiwuwa domin kamowa da hukunta masu hannu a harin.
Sanarwar da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar ta jaddada cewa ya zama tilas Gwamnatin Jihar Filato ta ɗauki tsauraran matakai tare da aiki da hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen wannan lamari ta yadda matakin zai zama izina ga wasu. Ya jaddada cewa “kowane ɗan Nijeriya yana da ’yancin zirgazirga a ko’ina a faɗin ƙasar ba tare da ƙaidi ba.”
Sakataren ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a Jihar Filato, Dakta Salim Musa Umar, ya yi Allah-wadai da harin, sa’annan ya buƙaci gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cikakken tsaron matafiya.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Kaduna, ya buƙaci gwamnatin Filato ta hukunta masu laifin da kuma yin adalci ga matafiyan, yana mai kira ga al’ummar jiharsa su kwantar da hankalinsu kada su ɗauki doka a hannnu.
ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya ta mika ta’aziyya game da lamarin a yayin da Gawmnan Filato, Caleb Mutfwang, ya ce babu dalilin far wa matafiyan, don haka, masu laifin za su fuskanci hukunci.
Mutum 22 sun shiga hannu
Rundunar ’Yan Sanda da ke Jihar Filato ta sanar da kama wasu mutum 22 bisa zargin hannunsu a harin. Mai magana da yawun rundunar, Alabo Alfred, ya ce a lokacin da suka samu labarin harin suka gaggauta tura jami’ansu, kuma sun yi nasarar tarwasta gungun fusatattun mutanen.
A cewarsa, jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da mutum 21 daga hannun mutanen suka kai su asibiti, inda ake jinyar su. “Bayan bincike mun gano cewa matafiyan sun fito ne daga yankin Zariya na Jihar Kaduna za su je ɗaurin auren ɗan uwansu a ƙaramar Hukumar ƙu’an Pan ta Jihar Filato. Amma da suka yi ɓatar hanya, sai gungun wasu mutane suka tsare motar suka sa mata wuta, wasu daga cikin fainsjojin sun rasu, wasu kuma suka jikkata,” in ji shi, yana mai gargaɗi, musamman ga matasa su guji ɗaukar doka a hannunsu.
Lokutan da aka kashe matafiya a Filato
An sha kai wa matafiya irin wannan hari a Jihar Filato.
A ranar 14 ga Agusta 2021, wasu zauna-gari-banza sun kashe matafiya 25 tare da jikkata wasu 14, a hanyarsu ta komawa Jihar Ondo, bayan sun kai wa Sheikh ɗahiru Bauchi ziyara a Jihar Bauchi.
Matafiyan sun gamu da ajalinsu ne a misalin ƙarfe 10:30 na safe a hanyar Gada-Biyu zuwa Rukuba da ke ƙarama Hukumar Jos ta Arewa.
Idan za a iya tuwana, kafin nan a ranar 30 ga watan Satumbar 2018 aka sanar da ɓacewar tsohon Shugaban Gudanarwa na Rundunar Sojin ƙasa ta Nijeriya, Manjo-Janar Idris Alkali (ritaya) a yankin DuraDu da ke ƙaramar hukumar ta Jos ta Arewa, a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.
Daga bisani rundunar sojin Nijeriya ta sanar cewa bayan bincike mai zurfi, ta gano gawarsa Manjo-Janar Alƙali a cikin wata tsohuwar rijiya da ke ƙauyen Guchwet a gundumar Shen da ke ƙaramar hukumar.
A ranar 16 ga watan Fabrairun 2022 kuma, wassu ɓata-gari suka tare hanya suka kashe wasu matafiya huɗu suka jikkata wasu da dama a Mahaɗar Bida Bidi da ke ƙaramar hukumar, a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Nasarawa daga Kano.
A yayin da ake ci gaba da shari’a kan kisan Manjo-Janar Idris Alƙali, har zuwa wannan lokaci dai babu wata ƙwaƙƙwarar magana game da batun matafiyan da aka kashe a Gada Biyu.