Wasu ’yan bindiga sun sake kai hari a kauyen Sayaya da ke Karamar Hukumar Matazu a Jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutum biyar.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata, sa’o’i 24 bayan harin da wasu mahara suka kai wa masu taron Mauludi, inda aka rawaito sun kashe akalla mutum 25.
- Gaza: Ba za mu tsagaita wuta ba sai… —Netanyahu
- Afirka ta Kudu ta janye dukkan jami’an diflomasiyyarta daga Isra’ila
Matazu da Musawa dai na makwabtaka da Karamar Hukumar ne inda wasu daga cikin wadanda harin masu Mauludin ya ritsa da su.
Wani mazaunin garin na Sayaya, wanda ya ce mahaifinsa na cikin wadanda aka kashe, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun kai farmaki gida-gida, inda suka kashe biyar tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Ya ce ’yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da dabbobi tare da kwashe wasu kayayyakin amfanin yau da kullum a yayin farmakin.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “A ranar 6 ga watan Nuwamba, 2023, ‘yan fashin daji dauke da muggan makamai irin su AK-47, sun kai hari Kauyen Sayaya, Matazu a jihar Katsina.
“Bayan samun rahoton nan take, jami’an tsaro suka wurin, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar tare da yin nasarar dakile harin.
“Duk da haka, an harbe mutum biyar, biyu sun jikkata, sannan maharan sun yi garkuwa da mutane biyar. An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Katsina a yayin da yake jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ya bukaci jama’a da su bada bayanan da za su taimaka wajen gudanar da bincike tare da zakulo maharan.
Hare-haren ‘yan bindiga na karuwa a kwanan nan a jihar Katsina duk da kirkiro jami’an sa ido da gwamnatin jihar ta yi a matsayin wani mataki na dakile matsalar.