✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Afirka ta Kudu ta janye dukkan jami’an diflomasiyyarta daga Isra’ila

Muna matukar damuwa da yadda ake ci gaba da kashe kananan yara da fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba.

Afirka ta Kudu ta sanar da janye dukkan jami’an diflomasiyyarta daga Tel Aviv bayan kazamin harin da Isra’ila ta kai a Gaza a daren Lahadi.

Harin bama-bamai dai na daya daga cikin mafi muni da Isra’ila ta yi tun bayan yakin da aka fara wata guda da ta wuce.

A cewar asibitin Al-Shifa na birnin Gaza, kimanin mutane 200 ne suka mutu.

Gwamnatin Afirka ta Kudu, wadda ta dade tana goyon bayan Falasdinawa, ta yi kakkausar suka ga Isra’ila a ranar Litinin

Ministan harkokin wajen kasar Naledi Pandor ya shaidawa taron manema labarai cewa, Afirka ta Kudu na janye jami’an diflomasiyyarta.

Pandor ya bayyana cewa: “Muna matukar damuwa da yadda ake ci gaba da kashe kananan yara da fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba a yankunan Falasdinawa, kuma mun yi imanin ramuwar gayyar da Isra’ila ke yi ya zama abin damuwa.

Har yanzu dai Isra’ila ba ta ce uffan ba game da wannan furuci na Afirka ta Kudu ba, amma ta dage cewa tana kokarin ganin ta rage asarar rayukan fararen hula tare da zargin Hamas da ke iko da zirin Gaza da yin amfani dda fararen hula a matsayin garkuwa.

A ranar 7 ga Oktoba, mayakan Hamas —wadanda Birtaniya da Amurka da sauran kasashen yammacin duniya suka ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci—sun kashe mutane fiye da 1,400 a Isra’ila.

Haka kuma sun yi garkuwa da mutane sama da 230 ciki har da wani dan kasar Afirka ta Kudu daya wanda har yanzu ba a tabbatar da sunansa ba.

A Lahadin da ta gabata ce Kasar Chadi ta sanar da yi wa jakadanta da ke Isra’ila kiranye sakamakon hare-haren da kasar ke kai wa Gaza.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta fitar a ranar Lahadi, ta yi Allah-wadai da irin yadda ake samun asarar rayuka a Gaza tare da kira kan a tsagaita wuta.

Chadi ce kasar Afirka ta farko da ta soma daukar irin wannan matakin daga nahiyar Afirka, duk da cewa tuni kasar Turkiyya ta dauki wannan matakin na yi wa jakadanta kiranye.

Haka ma kasashen Bolivia da Chile da Colombia da ke Kudancin Amurka tuni suka dauki matakin yanke dangantaka da Isra’ilar sakamakon ci gaba da kisan da take yi wa Falasdinawa.

Zanga-zangar kin-jinin Isra’ilar na ci gaba da kankama a kasashe da dama ciki har da Amurka da kuma Birtaniya.

Alkaluman da ma’aikatar lafiyar yankin Gaza ta fitar a baya bayan, sun nuna cewar Falasdinawa dubu 10,022 Isra’ila ta kashe, tun bayan hare-haren ramuwar da ta kaddamar kan harin da mayakan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe mutane fiye da dubu 1,400.

Tuni dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa kare fararen hula “Dole ya zama mai muhimmanci” a yakin da ake yi tsakanin Isra’ila da Falasdin, inda ya yi gargadi kan cewa Gaza na koma wa “makabartar yara kanana.”

Guterres ya shaida wa ’yan jaridu cewa “hare-hare ta kasa da sojojin Isra’ila ke kaiwa na ci gaba da ruwan bama-bamai kan fararen hula, asibitoci, sansanonin ‘yan gudun hijira, masallatai, cocina da wuraren ayyukan MDD – da suka hada da gidaje. Babu wanda ya tsira.”

Ya ce karara ana aikata laifukan take hakkokin da adam da dokokin kasa da kasa, kuma yana sake kira da a tsagaita wuta don samun damar taimaka wa mutane.