Gwamnatin Turkiyya ƙaƙashin jagorancin Shugaba Recep Erdogan ta sanar da dakatar da duk wasu harkokin kasuwanci da Isra’ila.
Ma’aikatar kasuwanci ta Turkiyya ta ce, matakin dakatar da “fitarwa da shigo da kayayyaki” tare da Isra’ila na da nasaba da ƙaddamar da mummunan hare-haren da ake kai wa jama’a a yankunan Falasɗinawa.
- Ta kai gawar wani ya sa hannu ta samu lamuni a banki
- Wanda ya yi takara sau 238 yana shan kaye yana fatar samun nasara
Sanarwar da ma’aikatar kasuwanci ta Turkiyya ta fitar ta ce “an dakatar da hada-hadar safarar kayayyaki da ake shigo da su da fitarwa da suka shafi Isra’ila, wanda ya shafi dukkan kayayyakin.”
Idan an tuna cewa, Turkiyya ta kasance mai sukar gwamnatin ƙasar Isra’ila ƙarƙashin jagorancin Firaminista Benjamin Netanyahu kan hare-haren da take kaiwa Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
A yayin da take magana kan matakin da ta ɗauka na dakatar da hada-hadar kasuwanci na baya-bayan nan, Turkiyya ta gindaya sharaɗi na cewa za ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙabawa lsrael idan ta zaɓi ba da agajin jin ƙai marasa iyaka ga Gaza.
Ma’aikatar kasuwanci ta Turkiyya ta ce “Turkiyya za ta aiwatar da waɗannan sabbin matakan da sauri har sai gwamnatin Isra’ila ta ba da damar kai agajin jin ƙai ba tare da tsangwama ba zuwa Gaza.”
Kasashen biyu na da adadin cinikin da ya kai Dala biliyan 6.8 a shekarar 2023.
A watan da ya gabata ne Turkiyya ta ƙaƙaba wa Isra’ila takunkumin kasuwanci saboda abin da ta ce Isra’ila ta ƙi amincewa da Ankara ta shiga ayyukan agajin jiragen sama na Gaza da kuma hare-haren da take kaiwa yankin.
Tun a ranar Alhamis, Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Isra’ila Katzsaid, ya ce Erdogan yana karya yarjejeniyoyin da aka ƙulla ta hanyar toshe tashoshin jiragen ruwa na shigo da kayayyaki da Isra’ila.