Ƙungiyar Hamas ta sanar da karɓar tayin tsagaita wuta a yaƙin Gaza kuma tuni ta soma nazarin sabuwar yarjejeniyar da aka gabatar mata.
Hamas wadda ta nuna alamun samun masalaha ta bayyana cewa manufar yarjejeniyar ita ce kawo ƙarshen hare-hare Isra’ila da janye dakarunta daga yankin.
- Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP
- 2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADC
Ƙungiyar ta ce tana tuntuɓar abokan shawararta, sannan ta jinjina wa ƙoƙarin masu shiga tsakanin.
Shugaban Amurka ne ya gabatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana 60, wadda ya ce tuni gwamnatin Isra’ila ta amince da ita.
To sai dai rahotonni na cewa da dama cikin ministoci masu ra’ayin riƙau ba su gamsu da ita ba, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya dage cewa yana son kawo ƙashen Hamas.