Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da ƙaddamar bincike a game da harin da dakarunta suka kai kan wata cibiyar intanet da ke yankin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗimbin fararen hula a jiya Litinin.
Hukumar kare lafiyar fararen hula ta Falasɗinu, ta ce wasu daga cikin makaman da Isra’ila ta harba a jiya Litinin sun faɗa kan kasuwar kwamfuta ta ‘Al-baqa’ da ke gaɓar teku da ke birnin Gaza, kuma a wannan cibiyar kaɗai mutane 24 ne suka rasa raukansu.
- Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 a Borno
- Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina
Ɗaya daga cikin masu magana da yawun rundunar sojin Isra’ila ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, tabbatas sun kai hare-hare kan wurare da dama da dakarun Hamas ke fakewa don gudanar da ayyukansu a Gaza, to amma sun ɗauki dukkanin matakan da suka wajaba domin taƙaita illolin farmakin ga fararen hula.
Ahmed al-Nayrab, mai shekaru 26 a duniya kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira da rayukansu a wannan farmaki, ya ce lokacin da aka kai harin, akwai ɗimbin mutane da suka haɗa da masu shan shayi da kuma waɗanda suka zo don samun sadarwar intanet.
Ahmed ya ci gaba da cewa, “abin da ya faru a wannan wuri ba ya da bambanci da kisan kiyashi”, yana mai cewa “a duk inda ka duba sassan gaɓoɓi ne da kuma gangar jikunan mutane ne, yayin da wasu daga cikin gawarwakin ke ci da wuta kana wasu ke kwance jina-jina’’.