Isra’ila ta bayyana shirin ƙulla hulɗa ta diflomasiyya da ƙasashen Siriya da Lebanon da suka daɗe ba sa ga maciji da juna a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan na zuwa ne bayan samun lafawar rikici tsakanin Isra’ila da Iran.
Kasar Isra’ila ta ce za ta ƙulla hulɗa da ƙasashen da suka daɗe suna zaman doya da man ja, amma ta ce babu batun tattauna makomar tuddan Golan da ta ƙwace daga hannun Siriya.
Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Saar wanda ya bayyana hakan a wannan Litinin din ya ce ƙasarsa tana da yaƙini kan karya lagon ƙasar Iran lokacin fito na fito na tsawon kwanaki 12 da suka yi a bayan nan.
Dangane da hakan ne Isra’ilan ke cewa za ta ƙara ƙulla hulɗa ta diflomasiyya da ƙasashen yankin.
A shekara ta 2020 Isra’ila da ƙulla hulda da kasashe da dama na Laraba na Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain gami da Maroko da ke zama karo na farko, bayan wadda Isra’ila ta ƙulla da Jordan a shekarar 1994, da kuma wadda aka fara yi da Masar a shekarar 1979.