✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaza: Ba za mu tsagaita wuta ba sai… —Netanyahu

Benjamin Netanyahu ya ce tsaron Zirin Gaza zai koma hannun Isra'ila

Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa za ta kwace gudanar da tsaro a yankin Falasdinawa na Zirin Gaza, bayan kurar yakin da suka kaddamar a yankin ta lafa.

Netanyahu ya bayyana haka ne bayan yakin da kasarsa ta kaddamar a Gaza ya kashe Falasdinawa sama da 10,000, ciki har da kanan yara sama da 4,000 a cikin mako hudu.

Netanyahu ya ce sojojinsa ba za su tsagaita luguden wuta da suke a Zirin Gaza ba har sai kungiyar Hamas ta sako mutanen da ta yi garkuwa da su daga Isra’ila.

Ya bayyana hakan ne duk da kiraye-kirayen da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres ya sha nanatawa na tsagaita wuta ga Gaza.

Gutteres, wanda ya kaddamar da gidauniyar tallafin Dala biliyan 1.2 domin Falasdinawa a Zirin Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Kudus, ya bayyana damuwarsa kan yadda ya ce ‘an mayar da Zirin Gaza makabarta ga kananan yara.’

Isra’ila ta hana shiga da mai Gaza, matakin da Guttteres ya ce na barazana ga rayuwar jariran da za a sanya a kwalba da ma marasa lafiyar da za a yi wa tiyata da wadanda suka dogara da na’urori domin ci gaba da rayuwa.

Kasashen duniya, musamman na Musulunci da Larabawa da sauransu dai na ta la’antar kisan gillar da Isra’ila take ci gaba da yi a Gaza, inda ta kashe dubban fararen hula a asibitoci da makarantu da sansanonin ’yan gudun hijira.

Kawo yanzu Isra’ila ta raba miliyoyin Falasdinawa da gidajensu da ta yi lebur da su da bama-bamai, baya ga kisan gilla da take ci gaba da yi wa Falasdinawa a Gaza da sunan yaki da kungiyar Hamas da ta kai mata hari a ranar 7 ga watan Oktoba.