✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tottenham ta yi rashin nasara wasa uku jere a Firimiyar Ingila

Tottenham ta sha kashi a gida a hannun Chelsea da ci 4-1 ranar 6 ga watan Nuwamba.

Tottenham ta yi rashin nasara wasa na uku a jere a Firimiyar Ingila, bayan da Aston Villa ta doke ta 2-1 ranar Lahadi a wasan mako na 13.

An dai ci Tottenham din ce gida, wadda take jimamin mutuwar tsohon dan wasanta Terry Venables, wanda ya horar da ita.

Tsohon dan wasan tawagar Ingila, an sanar da mutuwarsa awa biyu kan take leda a wasan na mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Hakan ya sa aka yi shiru a filin kan fara wasan, domin girmama wanda ya buga wa Tottenham wasa dagga 1966 zuwa 1969.

Ya kuma lashe FA Cup a kungiyar a 1967 da kuma a matakin kocin Tottenham a 1991.

Minti na 22 da take leda Tottenham ta ci kwallo ta hannun Giovani Lo Celso, amma daf da hutu Aston Villa ta farke ta hannun Pau Torres, sannan ta zura na biyu a raga ta wajen Ollie Watkins.

Bayan da aka kammala buga wasannin mako na 10, Tottenham tana ta daya a kan teburi, amma yanzu ta koma ta biyar, Aston Villa ta yi sama zuwa mataki na hudu bayan mako na 13.

Wasa na uku a jere da aka doke Tottenham, wadda ta sha kashi a gida a hannun Chelsea da ci 4-1 ranar 6 ga watan Nuwamba.

Haka kuma ranar 11 ga watan Nuwamba Wolverhampton ta ci Tottenham 2-1 da wanda Aston Villa ta yi nasara da 2-1 ranar 26 ga watan Nuwamba.

Watakila Tottenham ta ci gaba da yin kasan teburi, bayan da za ta ziyarci Manchester City ranar 3 ga watan Disamba sannan ta karbi bakuncin West Ham ranar 7 ga watan Disamba.

Wasa na uku da ke gabanta shi ne wanda za ta fafata da Newcastle United a gida a wasan mako na 16 a Firimiyar ranar 10 ga watan Disamba.