✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon kocin Ingila Terry Venables ya rasu

Venables ya jagoranci kungiyar Tottenham da Crystal Palace da Australiya.

Tsohon kocin Ingila Terry Venables ya rasu a cewar wata sanarwa da iyalansa suka fitar a wannan Lahadin ta tabbatar.

Venables ya rasu yana da shekara 80 kuma shi ya jagoranci tawagar kwallon kafa ta Ingila zuwa gasar Euro 96 inda har Ingilar ta kai zagayen kusa da na karshe.

Haka kuma tsohon kocin shi ya jagoranci Barcelona zuwa wasan karshe na Gasar Cin Kofin Turai a 1986. Muna matukar bakin ciki da rashin miji da uba nagari wanda ya rasu jiya bayan doguwar jinya,” in ji iyalansa.

“Za mu nemi a ba mu dama domin a wannan lokaci mai cike da bakin ciki don nuna alhinin rashin wannan mutum da muke kauna da muka yi sa’ar samu a rayuwarmu,” in ji iyalansa.

Baya ga Ingila da Barcelona, Venables ya jagoranci kungiyar Tottenham da Crystal Palace da Australiya.

Marigayin ya shahara tun a shekarun 1960 a lokacin da ya buga wa kungiyoyin Chelsea da Totteham da Queens Park Rangers wasa.