Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana.
A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu.
- ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’
- Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas
Inter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya.
A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna 120, Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara ci wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona, daga baya Eric Garcia da Dani Olmo da Raphinha suka rama ƙwallayen har da ƙari.
Sai dai ana dab da tashi ne kuma Francesco Acerbi mai shekaru 37 ya rama wa Inter ƙwallo ta uku, abin da ya tilasta wasan zuwa ƙarin lokaci.
A minti na 99 ne Davide Frattesi ya ci wa Inter Milan ƙwallon da ya ba ta nasara.
Ƙungiyar wadda a yanzu Simone Inzaghi ke jagoranta, ta kai wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai karo na biyu ke nan a cikin shekaru uku.
Yanzu Inter Milan za ta haɗu ne da PSG ko Arsenal waɗanda za su fafata nasu wasan a ranar Laraba.