✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa zai cire wa Real Madrid kitse a wuta?

A yau Lahadi, Madrid za ta fafata da Celta a Santiago Bernabeu a wasan mako na 34 a gasar La Liga.

Duk da nasarorin da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu a kakar 2023/24 na lashe kofuna 5, ciki har da Kofin Zakarun Turai, amma tana fuskantar ƙalubale a kakar bana, inda ake ganin da wahala ta iya lashe wani kofi bayan Super Cup da ta ci a farkon kaka, da ta ƙwace a hannun Atlanta da ci 2-0 a filin kwallon kafa na National Stadium Warsaw da ke Poland.

Magoya baya na zargin Ancelotti da rusa kungiyar

Magoya bayan Real Madrid da dama sun yi a manna cewa kwai laifin mai horarswa Carlo Ancelotti, duk da tarin nasarori da ya jagornaci kungiyar ta samu a kaka uku da suka wuce, ciki har da lashe Kofin Zakarun Turai 2 da Laliga 2, baya ga wasu kananan kofuna guda hudu — Super Cup guda biyu da King Cup da kuma Club World Cup.

Amma duk da haka wasu magoya bayan kungiyar ba su gamsu da kamun ludayinsa ba a wannan kakar inda suke ganin ba ya ba wa matasa dama su baje basirarsu, ya fi fiifta ’yan wasan da suka fi shahara a kugiyar.

Da wannan ne wasunsu suke gani kamar kocin ya jahilci sabon sauyin da harkar kwallon kafa ta samu na amfani da matasa masu tasowa a sha dayan farko.

Brazil na neman Ancelotti ido rufe

A kwanakin bayan an yi ta rade-radin cewa Real Madrid na kokarin raba gari da Ancelotti, amma dai da har yanzu babu wani rahoto mai karfi da ke tabbatar da hakan.

Amma wasu rahotanni sun ce Ancelotti mai shekarau 65 zai ci gaba da tattaunawa kan karbar aikin horar da tawagar ’yan wasan kasar Brazil kafin watan Yuni, inda zai gana da wakilan Hukumar Kwallon Kafar Brazil (CBF).

Game da batun makomarsa Brazil, Ancelotti dan asalin Italiya, ya ce “za ci gaba da a tattaunawa a makon gobe.”

Ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar bayan da Barcelona ta casa Real Madrid ta lashe Copa del Rey a Sevilla.

Hakazalika, an gani hangi attajirin nan dan kasar Brazil, Diego Fernandes, wanda ke wakiltar Hukumar CBF ya halarci wasan El Clasicon da aka yi a Sevilla, kuma fahimci cewar ziyayar ta Fernandes zuwa Turai, na da alaka da lallashin kocin na Real Madrid ya karbi horas da tawagar CBF da zarar an kammala kakar Sifaniya.

Ke nan idan sun daidaita, akwai yiwuwar Ancelotti zai bar Real Madrid kafin gasar Club World Cup da za a yi a Amurka a bana.

A halin da ake ciki Ancelotti shi ne kan gaba a jerin masu horaswa da Brazil ke fatan dauka, domin maye gurbin Doribal Junior, wanda ta kora bayan da Argentina ta caskara kasar da ci 4-1 a Buenos Aires a watan jiya.

Brazil tana mataki na hudu a teburin Kudancin Amurka a wasannin neman shiga Gasar Kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Kanada da kuma Medico.

Duk da cewa ba ta fuskantar barazarar kasa zuwa babbar gasar ta duniya, Brazil ta ta yi amannar cewar Ancelotti ne kadai zai kai ta ga kara lashe kofin.

Tun kafin a fara Copa America a bara, Brazil take ta zawarcinsa, amma hakarta bai cimma ruwa ba.

Wa zai maye gurbin Ancelloti?

Ana sa ran idan har Real Madrid ta rabu da Ancelotti za ta maye gurbinsa da tsohon dan wasanta na tsakiya, Xabi Alonso, wanda yanzu shi ne kocin Bayer Leverkusen.

Alonso ya yi nasarar lashe Kofin Bundesliga a kakar 2023/2024 a Kungiya Bayer Leverkusen tare da kafa tarihin buga wasa 52 ba tare da an duke su ba, wanda ke ciikin abubuwan da sa yake kamshin turaren dan goma ga kungiyoyi da dama.

Sai dai kuma Xabi ya watsi da duk wani tayi da ke gabansa, yana mai sa ran amsar tayin Real Madrid kadai.

Amma wasu rahotonni sun nuna Real Madrid din tana kwadayin tsohon kocin kuniyar kwallon kafa ta Liverpool dan kasar Jamus, Jurgen Klopp.

Duk da cewa har yanzu ba a ji daga bakin bangarorin biyu ba, amma ga dukkan alamu kungiyar ta fi mayar da hankali a kan tsohon dan wasanta na tsakiya Xabi Alonso.

Raunin ’yan wasa: Madrid ta ji a jikinta

A wannan kakar Madrid ta yi fama da kalubalen samun raunin ’yan wasa, inda tun a farkon kaka ’yan wasan bayanta biyu na sha dayan farkon suka ji mummunar raunuka — Cikinsu har da Mataimakin Kyaftin dinta dan kasar Sifaniya, Dani Carvajal da kuma Eder Militao dan kasar Brazil.

Tuni dai daman David Alaba yana fama da jinya na tsawon lokaci.

Wannan yanayi ya sa kungiyar ta wayi gari ba ta da zabi face ta dinga sirka ’yan wasan baya dana tsakiya a wasannin da ta doka a wannan kakar.

’Yan kwallon Faransa na tsakiya Tchuameni da Camabinga da kuma dan tsakiya Balberde ne yanzu suke bada gudunmawa a baya.

Kalubalen da ke gaban Real Madrid a bana

Real Madrid tana bukatar maki 15 a wasannin da suka rage mata a gasar La Liga a kakar 2024/25.

A halin da ake ciki, Real Madrid mai rike da La Liga na bara tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki hudu tsakaninta da Barcelona da ke saman teburin.

Da ma tuni Arsenal ta yi waje da ita a Gasar Zakarun Turai, yayin da Barcelona ta lashe Spanish Super Cup ta kuma kwace Copa del Rey daga hannunta a kakar nan.

A yau Lahadi, 4 ga watan Mayu za a fafata tsakaninta da Celta a Santiago Bernabeu a wasan mako na 34 a gasar La Liga.

A wasan farko da suka buga watan Oktoban 2024 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu, Barcelona ce ta yi nasarar cin 4-0.

Ranar Lahadi 11 ga watan Mayu za a fafata a wasan hamayya na El Clasico inda kungiyar da Carlo Ancelotti da ke rike da kambu za ta je gidan Barcelona a wasan a mako na 35.

Daga nan za ta fafata a sauran wasannin La Liga uku da za su rage mata, inda za ta karbi bakuncin Mallorca, sannan ta je Sebilla ta karkare da Sociedad a gida.

Bayan kammala wasannin Gasar La Liga na bana, Real za ta buga Club World Cup da za ta fara wasan farko da Al Hilal ranar 18 ga watan Yuni a Amurka.

Wasannin da suka rage mata a bana

  • Real Madrid – Celta, La Liga mako na 34 (Lahadi 4 ga Mayu).
  • Barcelona – Real Madrid, La Liga mako na 35 (Lahadi 11 ga Mayu).
  • Real Madrid – Mallorca, La Liga mako na 36 (Litinin 14 ga Mayu).
  • Sevilla – Real Madrid, La Liga mako 37 (Alhamis 17 ko 18 ga Mayu).
  • Real Madrid – Sociedad, La Liga mako na 38 (Alhamis 24 ko 25 ga Mayu).