✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 10: Me ya sa Kofin Zakarun Turai ya gagari Barcelona?

Shekaru 10 ke nan Barcelona ba ta sa hannu a kan Kofin Zakarun Turai ba.

A Talatar makon jiya ce Inter Milan ta ƙara lalata wa Barcelona mafarkinta na ɗaukar Kofin Zakarun Turai a shekaran nan, bayan an yi kare-jini-biri-jini tsakanin kungiyoyin guda biyu a wasan kusa da na karshe.

An tashi wasan ne da ci 4-3 a San Siro gidan Inter Milan bayan sun yi 3-3 a gidan Barcelona.

Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara zura wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona.

Davide Frattesi ne ya ci ƙwallon da ta bai wa Inter nasara a cikin ƙarin lokaci, bayan ƙwallon ne kuma aka kaure da ruwan sama.

Barça, wadda a haduwar farko, ta taso daga ci biyu da nema da aka yi mata, inda ta daidaita lamarin zuwa 3-3, ta sake yunkurowa, ta sauya sakamakon wasan, inda har aka ga alamun za ta samu zuwa wasan karshe na gasar a karon farko bayan shekarar 2015, amma sai al’amari ya sauya.

Lokacin da Raphinha ya ci kwallo a minti na 87, bayan da Eric García da Dani Olmo suka farke ƙwallayen da Lautaro Martínez da Hakan Çalhanoglu suka ci kafin hutun rabin lokaci, Barcelona ta zamto a kan gaba a karon farko a haduwar tasu, amma a cikin minti shida kacal, sabon dan wasan bayan Inter, Francesco Acerbi, wanda rabonsa da cin kwallo tun a watan Afrilun 2023 ya saka musu ƙwallo a minti na 93.

Barcelona ba ta farke wannan kwallo ba har aka tashi wasa 4 da 3, wasan da ake wa kallo a matsayin daya daga cikin wasannin kusa da na karshe mafiya armashi a Gasar Zakarun Turai.

Yanzu dai Barcelona ta yi waje, Inter kuma ta samu zuwa wasan ƙarshe.

Tarihi ya maimaita kansa

A shekara ta 2010 Inter Milan ta taba cire Barcelona a irin wannan matakin na kusa da wasan karshe, sai dai akwai bambancin zira kwallaye a raga.

A wancan lokacin an buga wasan farko ne a gidan Inter Milan, inda ta doke Barcelona da ci 3-1.

Tun farko dai Barcelona ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Pedro a minti 19, inda Sneijer ya farke a minti 30, bayan an je hutun rabin lokaci, an dawo ne Inter ta kara biyu ta hannun Maicon da Milito, a haka aka tashi wasan.

Inter karkashin jagorancin Jose Mourinho a wancan lokacin ta sha da kyar a gidan Barcelona, wadda Pep Guardiola ke jan ragama, bayan an zagayo, inda tun a minti 28 aka ba wa dan kwallon Inter na tsakiya, Thiago Motta jan kati.

Hakan ya sa Mourinho shiga wani yanayi, inda ya mayar da ’yan wasansa gaba daya baya, banda lamba 9, wato Militao.

Kwallo daya Barcelona ta iya farkewa ta hannun dan kwallon bayan ta Gerard Pikue, a haka aka tashi daga wasan Inter ta yi nasara da ci 3-2 gida da waje.

Shekara 10 babu kofin Zakarun Turai

Duk da wannan kakar, shekaru 10 ke nan Barcelona ba ta sa hannu a kan Kofin Zakarun Turai ba, tun wanda ta ci a hannu kungiyar kwallon kafa ta Italiya, wato Juventus da ci 3-1 a shekara 2015, wasan da Barcelona ta ci kwallaye ta hannun Rakitic da ’yan wasan gabanta Neymar da suarez.

Tun daga lokacin Barcelona ke samu koma baya a Gasar Zakarun Turai, inda ta buga wasan kusa da na karshe sau 2, na daf da na kusa da na ƙarshe kuma sau 3, sai zangon ko ta kwana sau 3, ragowar biyun tun a zagayen rukuni aka cire ta.

Shaharar Barcelona: Yanzu aka fara?

Duba da yadda Barcelona ta taka rawar gani a wannan kakar da matasan ’yan kwallo irin su Pedri da Cubarsi da Fermin Lopez, musamman matashin ɗan ƙwallon gabanta ɗan shekara 17 Lamine Yamal, za a ga kusan yanzu aka fara ƙwallon.

Wani masanin kwallon kafa kuma cikakken magoyin bayan Barcelona ya tabbatar mana da cewa, tunda ba su kawo kofin ba wannan kakar, shekara mai zuwa ba abin da zai hana Barcelona dauka.

Inda ya nuna amincewa da sabon salon da mai horar da kungiyar, Hansi Flick ya dauko don ganin ya kai kungiyar ga kokoluwar nasara.

Ya kara da cewa, lallai shi a wannan karon, babu wani dan wasan Barcelona da ya zaga ko ya daura wa laifin cire su da aka yi a Gasar zakarun Turai, don a ganinsa kowa ya buga abin da ya dace kawai sa’a ce ba su da ita.

A karshe kuma ya kara da jaddada wa ’yan adawansu a tari gaba.