✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai

PSG da Barcelona sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe duk da rashin nasara da ƙungiyoyin biyu suka yi a ranar Talata.

Paris St Germain ta kai zagayen daf da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai duk da rashin nasara da ta yi a hannun Aston Villa ranar Talata a Villa Park.

Aston Villa ta yi nasarar cin PSG 3-2, inda Tielemans da McGinn da kuma Konsa suka ci mata ƙwallayen a wasa falle na biyu a zagayen kwata fainal.

Ita kuwa ƙungiyar ta Faransa ta ci nata ƙwallayen ta hannun Hakimi da kuma Nuno Mendes.

PSG ta kai zagayen gaba da cin 5-4 gida da waje jimilla, bayan da ta yi nasarar cin 3-1 a makon jiya a Faransa.

Ita ma Barcelona da ke buga gasar La Liga ta kai matakin daf da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana duk da shan kashi da ta yi a hannun Borussia Dortmund.

Dortmund dai ta taka wa Barcelona burki, bayan wasa 24 a jere ba tare da rashin nasara ba a dukkan kaka a bana.

Ƙungiyar ta Jamus ta doke ta Sifaniya da 3-1 a wasa falle na biyu na Gasar Zakarun Turai zagayen kwata fainal da suka fafata a Jamus ranar Talata.

Duk da haka Barcelona ta kai zagayen daf da ƙarshe sakamakon cin 5-3 gida da waje jimilla, bayan da ta ci 4-0 a makon jiya a Sifaniya.

Serhou Guirassy ne ya ci wa Dortmund ƙwallo uku rigis, wanda ta farko a bugun fenariti, sannan ya ƙara biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Barcelona ta zare ɗaya ne ta hannun Ramy Bensebaini, ɗan wasan Dortmund da ya ci gida.

Rabon da Barcelona ta yi rashin nasara tun cikin Disamba, bayan da Atletico Madrid ta ci ta 2-1, daga nan ta yi karawa 24 a jere ba tare da rashin nasara ba har da canjaras huɗu daga ciki.