✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

United ta yi raga-raga da Everton a Goodison Park

Karo na 17 kenan da Anthony Martial da Marcus Rashforrd suka ci kwallo a tare a Premier League.

Manchester United ta je bakunta Goodison Park ta doke Everton 3-0 a wasan mako na 13 a Premier League ranar Lahadi.

Minti uku da fara wasa ne United ta zura kwallo ta hannun Alejandro Garnacho haka suka je hutu, United tana da daya a raga.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Marcus Rashford ya kara na biyu a bugun fenariti, sannan Anthony Martial ya kara na uku a raga.

Karo na 17 kenan da Anthony Martial da Marcus Rashforrd suka ci kwallo a tare a Premier League, masu bajintar sune Scholes da Ruud Van Nistelrooy masu 19.

United ta buga karawar ba tare da koci, Erik ten Hag ba, wanda ke hukuncin dakatarwa, an kuma sa matashi mai shekara 18 a karawar, Kobbie Mainoo.

Da wannan sakamkon United tana ta shidan teburi mai maki 24 da tazarar shida tsakaninta da Arsenal, wadda ke jan ragamar teburin.

Ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, United za ta ziyarci Galatasaray domin buga Champions League karawar cikin rukuni.

Daga nan Newcastle United za ta karbi bakuncin Man United a wasan mako na 14 a Premier League ranar Asabar 2 ga watan Disambar 2023.