✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai gabatar da kasafin kudin badi na N27.5tr ranar Laraba

Wannan ne cikakken kasafi na farko da Tinubu zai gabatar wa majalisar tun bayan rantsar da shi a watan Mayu.

Majalisar Zartarwa ta amince da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2024.

Dangane da hakan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar wa Majalisar Tarayya kasafin a ranar Laraba mai zuwa.

Sakataren bincike da yada labarai a Majalisar Tarayya, Dokta Ali Barde Umoru ya tabbatar da haka a yammacin yau.

A kunshin kasafin da Majalisar Zartarwar ta amince da shi, an tsaida farashin gangar mai a kan $73.96 da lissafin cewa za a rika hako ganguna miliyan 1.78 a rana da kuma farashin duk dala guda a kan N750.

Wannan ne cikakken kasafi na farko da Bola Tinubu zai gabatar wa majalisar tun bayan rantsar da shi a watan Mayun da ya wuce.

Gabatar da kasafin ya nuna cewa Mista Tinubu zai ci gaba da tafiyar da tsarin kasafin kudin daga Janairu zuwa Disamba kamar yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar.