Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya soke ziyarar aiki da ya shirya zuwa Kaduna, a maimakon haka zai ziyarci Jihar Benuwe domin jajanta wa al’umma sakamakon kashe-kashen da aka samu a jihar a baya-bayan nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.
- Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku
- Tinubu ya bayar da umarnin binciken hare-haren Benuwe
Kakakin ya ce Shugaba Tinubu zai kai ziyarar ce a ranar Laraba domin duba halin da jihar ke ciki bayan kashe-kashen da aka samu a ’yan kwanakin nan a jihar.
Haka kuma, a yayin ziyarar, shugaba Tinubu zai gana da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da sarakuan gargajiya da ’yan siyasa da jagororin addini da shugabannin al’umma da kungiyoyin matasa, da nufin lalubo hanyoyin magance rikicin jihar.
Tuni dai shugaban ya aike da tawagar wakilan Gwamnatin Tarayya a yau da ta ƙunshi Sakataren Gwamnatin Tarayya da Babban Sufeton ’yan sanda da shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri ta ƙasa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da shugabannin kwamitsocin tsaro a majalisun dokokin ƙasar.
Fadar shugaban kasar ta ce wata babbar tawagar manyan jami’an tsaron Nijeriya ta isa Jihar Benuwe domin bayar umarnin yadda za a tunkari matsalar rashin tsaron da jihar ke fuskanta da kuma mai do da kwanciyar hankali.
A ƙarshen mako ne dai aka samu munanan hare-haren da suka yi sanadin kashe fiye da mutum 100 a Jihar Benuwe.