A yau ne Najeriya ke bikin ranar Dimokuraɗiyya, wanda masana siyasa a ciki da wajen ƙasar ke jinjina kan yadda aka kwashe shekara 26 kan tafarkin mulkin farar hula.
Najeriya, ta kasance ƙasa mafi yawan al’umma a Nahiyar Afirka inda ake bikin murnar ranar dimokuraɗiyyar domin tunawa da zaɓen 12 ga watan Yuni wanda ake ganin shi ne zaɓe mafi inganci da aka taɓa gudanarwa a Najeriya.
- NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya?
- An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato
Hakan dai na zuwa ne duk kuwa da cewa an soke zaɓen, lamarin da ya haifar da taƙaddama da ruɗani game da zaɓen.
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya sauya bikin ranar dimokuradiyyar daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin karrama wanda ake da yaƙinin shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar na 1993, wato Moshood Abiola.
Hakan dai na nufin Najeriya ta kwashe shekara 26 tana kan tafarkin mulkin farar hula dimukuraɗiyya ba tare da katsalandan na sojoji ba.