Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.
Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa da tsaki a Jihar Kano.
- Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu
- Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71
A cewarsa, Tinubu ya yi watsi da halin da yankin arewacin ƙasar ke ciki wajen gina Kudancin Najeriya da kuma samar musu da kayan more rayuwa.
“Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan,” in ji Kwankwaso.
Kwankwaso wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023, ya zargi jam’iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Nijeriya.
Ya ce: “Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi,” in ji Kwankwaso.
Ya ce wannan ya sa ake fama da rashin tsaro da talauci da sauransu.
Kwankwaso wanda ke jawabi wajen taron sauraron ba’asin jama’a a kan yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, ya ce abin takaici shi ne tamkar gwamnatin ta karkata kasafin kudin ƙasar ne baki daya zuwa bangare guda.
Tsohon gwamnan ya bayyana takaici a kan lalacewar hanyar Abuja zuwa Kano, musamman jiya da ya koma gida ta mota, bayan kamfanin jirgin da zai shiga ya sauya lokacin tashi daga yamma zuwa cikin dare.
Kwankwaso ya ƙara da cewar, akasarin hanyoyin da ke Arewacin Najeriya sun lalace, amma kuma gwamnatin APC na zuba maƙudan kudade zuwa gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa da more rayuwa a Kudancin ƙasar.
Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sauya alƙibla domin tafiya da kowa da kuma tabbatar da cewa an raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin ci gaban dukkan sassan ƙasar.
“Yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnati ta kawo sauyi, domin mu san cewa ba gwamnati ce kaɗai ta wani ɓangare guda ba,” in ji shi.