✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai kai ziyara Kano gobe Juma’a

An buƙaci Kanawa da su yi wa shugaban ƙasar kyakkyawar tarba cikin karamci da mutuntawa.

Gwamnatin Kano ta shirya karɓar baƙuncin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a gobe Juma’a.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yammacin wannan Alhamis ɗin.

Sanarwar ta ambato Gwamna Abba Kabir Yusuf yana yi wa shugaban ƙasar maraba yayin da zai ziyarci jihar domin ta’aziyyar attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Alhassan Dantata da ya riga mu gidan gaskiya a makonnin da suka gabata.

Gwamna ya buƙaci Kanawa da su yi wa shugaban ƙasar kyakkyawar tarba cikin karamci da mutuntawa.