Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce kawo yanzu gwamnatinsa ta aiwatar da kashi 85 cikin 100 na alƙawuran da ta yi wa al’ummar jihar, kashi 15 ne kawai ya rage yayin da ya shiga kashi na biyu na mulkinsa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da sabon Shugaban ma’aikatansa, Dakta Sulaiman Wali Sani da babban Darakta a hukumar kula da ayyuka na musamman, Manjo Janar Sani Muhammad (Mai ritaya) da masu ba shi shawara na musamman guda 11 a ranar Alhamis.
- Ɗaliban Jami’ar KWASU 18 sun tsallake rijiya da baya a gobarar mota
- Sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga a Filato
Ya yi nuni da cewa, an cimma wannan nasarar ne bayan da aka yi nazari sosai kan ayyukan gwamnatinsa a cikin shekaru biyu da suka gabata.
“Na yi farin ciki da cewa a makon da ya gabata da na duba wurin rumfar zabenmu, duk alƙawuran da muka yi wa jama’a sun ragu a cikin shekaru biyu, mun aiwatar da kashi 85 cikin 100, don haka ina da sauran shekara biyu, a wannan ragowar kashi 15 ne za mu aiwatar da sauran.
“Yanzu mun gabatar da batun a gaban Majalisar Zartarwa ta Jiha, muna da kashi 15 cikin 100 ne kawai kuma muna da shekaru biyu. Don haka muna duban yanayi uku,” in ji shi.
Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa, gwamnati ba za ta huta ba, sai dai ta ci gaba da ɓullo da sabbin tsare-tsare don zurfafa tasirinta ga rayuwar jama’ar Kano.
“Muna kawo sabbin tsare-tsare da ayyuka waɗanda da yardar Allah SWT za su ci gaba da yin tasiri ga rayuwar al’ummar jihar nan, don haka ba za mu iya gudanar da hakan mu kaɗai ba, dole ne mu yi shi da ku duka,” in ji shi.