✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu sake gina kasuwar waya ta Farm Center — Abba

Ba kasuwa kawai za mu gina ba, cibiyar kasuwanci za mu gina domin jawo ’yan kasuwa daga ƙasashen duniya.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center da ta yi gobara a kwanakin baya.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce bayan ziyarar gani da ido da gwamnan ya yi a ranar Juma’a, ya ɗauki matakin sake gina kasuwar tare da sabunta ta da zamanantar da ita, aikin da da ya ce “gwamnan zai kashe naira biliyan 2.”

“Wannan yunƙuri ba kawai saboda gobarar ba ce, za mu yi amfani da wannan damar ne domin inganta tattalin arzikin jihar, da samar da ayyukan yi,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta saya ƙarin fili domin faɗaɗa kasuwar, inda za ta samu damar gina abubuwan da ake buƙata a kasuwa na zamani, ciki har da gina sashen masu kashe gobara domin jiran kar-ta-kwana.

“Ba kasuwa kawai za mu gina ba, cibiyar kasuwanci za mu gina domin jawo ’yan kasuwa daga ƙasashen duniya,” in ji shi.

A makonnin da suka gabata ne dai gobara ta tashi a kasuwar wacce aka yi ƙiyasin ta ƙone shaguna sama da 300 tare da janyo wa ’yan kasuwa asarar miliyoyin Naira.