✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano

Mutumin ya rasu bayan da aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano

Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu ƙwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daba masa wuta.

Bayanai sun nuna cewa barayin sun ritsa shi ne a yankin unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso, inda suka sossoke shi da wuka a ciki kuma suka kwace wayarsa, a ranar Laraba.

BBC ya ruwaito mutumin ya rasu bayan da aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, a ranar Juma’a.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jami’ar (NASU), Kwamared Bashir Muhammad, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da sauran hukumomi da su ɗauki tsattsauran mataki a kan kisan.