✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya hana Ganduje zuwa tarbar Tinubu a Kano

Ganduje ya na da masaniya kan ziyarar Tinubu kuma ya yi niyyar zuwa amma duk ƙoƙarin da ya yi domin ya samu damar halarta bai…

A bayan nan dai ana ci gaba da cece-kuce kan rashin ganin tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje a wurin tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin ziyarar da ya kai Jihar Kano a ranar Juma’a.

Ana dai ta rade-radin cewa sauka daga mukamin shugabancin jam’iyyar da ake zargin Ganduje ya yi ba da son ransa ba ne ya sanya ya yi watsi da shiga cikin kusoshin gwamnati da jiga-jigan ’yan siyasar da suka karbi bakuncin shugaban kasar a Kano.

Sai dai wani makusancinsa, Muhammad Garba, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce tsohon Gwamnan Kanon bai samu damar shiga sahun masu tarbar shugaban kasar ba ne saboda balaguron da zai yi zuwa birnin Landan.

A cewar Muhammad Garba, Ganduje wanda ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya a watan Yuni ya shirya tafiyar ne kwana biyar kacal da saukarsa daga muƙamin.

“Ba kamar abin da ake yaɗawa ba cewa da gangan ya ƙi zuwa ko kuma ba shi da lafiya, Ganduje ya je Landan ne saboda tafiyar da aka shirya da daɗewa tun kafin ziyarar,” in ji sanarwar.

Garba ya tabbatar cewa an sanar da Ganduje game da ziyarar shugaban ƙasar, “kuma ya yi niyyar zuwa amma duk ƙoƙarin da ya yi na sauya lokacin tashin jirginsa bai yi nasara ba”.

“Sauka daga muƙamin da Ganduje ya yi bai shafi alaƙarsa da Tinubu ba ko kaɗan, wadda ta ginu tsawon shekaru cikin girmamawa da buƙata irin ta siyasa,” a cewar Garba.

Garba wanda tsohon kwamashinan yaɗa labarai ne a gwamnatin Ganduje, bai bayyana abin da mai gidan nasa ya je yi Landan ba.

Aminiya ta ruwaito ziyarar da Tinubu ya kai Kano a ranar Juma’a domin yin ta’aziyyar attajirin dan kasuwar nan, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata wanda ya riga mu gidan gaskiya a ƙarshen watan jiya na Yuni.