✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A tsananta hukunci kan masu dukan mata — Sarki Sanusi

Abin takaicin da muke gani a yau shi ne yadda ake yi wa mata jina-jina da sunan ladabtarwa.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a tsananta hukunci kan masu cin zarafin ’ya’ya mata, yana mai cewa babu wani musulmi nagari da zai yi wa matarsa dukan da har zai yi mata lahani.

A yayin da yake tunatar da malamai da limamai kan muhimmiyar gudunmawar da za su bayar a wannan fage domin yi wa tufkar hanci, Sarkin ya bayyana damuwa kan yadda matsalolin fyade da kuma samun magidantan da ke dukan matansu suka zama ruwan dare a Jihar Kano.

Sarki Sanusi na wannan furuci yayin da ya karbi bakuncin tawagar cibiyar bunkasa bincike (dRPC) da kuma cibiyar nazarin addinin musulunci ta Jami’ar Bayero da ke Kano (CCID) suka kai ziyara fadarsa ta Gidan Rumfa a birnin Dabo.

A cewar Sarkin, “ban zan taba goyon dukan mace ba, kuma duk masu yi, suna yi ba da niyyar ladabtarwa ba. Amma abin takaicin da muke gani a yau shi ne yadda ake yi wa mata jina-jina da sunan ladabtarwa.

“Musulunci yana fifita mata da daraja fiye da kowane addini kuma duk masu neman fakewa a karkashinsa don cin zarafinsu, ba su ma fahimci addinin ba.

“Duk wanda yake dukan matarsa har ya yi mata rauni ba mutumin kirki ba ne, kuma ba ni na fadi haka ba, Annabi Muhammad (SAW) ne ya fada, wadanda ba su karanta ba ne ba su sani ba.”