Ana fargabar cewa wasu ɗalibai biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan wani farmaki da wasu ’yan uwansu ɗalibai suka kai musu a wata makarantar sakandire ta gwamnati da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11;30 na dare a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da wasu ɗaliban makarantar suka yi wa wasu ’yan uwansu ɗalibai huɗu rubdugu kan zargin neman maza a tsakaninsu.
- SEC za ta binciki kamfanonin ‘ponzi schemes’ 79 da ke zambatar ’yan Nijeriya
- Yadda za a ci gaba da zaman karɓar gaisuwar Buhari
“Da farko mun ɗauka ko rigima ce ta kaure a tsakanin ɗaliban biyu da suka riga mu gidan gaskiya, sai daga bisani muka fahimci cewa ana zargin an kama su ne suna neman juna kuma aka soma dukansu har ta kai ga sun ce ga garinku nan yayin da aka garzaya da wani ɗalibi ɗaya da ya jikkata.
“Amma tun a jiya [Talata] Kwamishinan Ilimi da wasu jami’ai daga ma’aikatar ilimi ta jihar sun ziyarci garin kuma ya umarci shugaban makarantar da a kafa kwamitinin gudanar da bincike kan lamarin.”
Kazalika, wata majiya a yankin ta ce ɗalibai biyu ne suka jikkata kuma a halin yanzu suna samun kulawa a Babban Asibitin Bichi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa a halin yanzu mutum 11 da ake zargi da hannu a lamarin sun shiga hannu.
Ita ma Gwamnatin Kano ta bakin Kwamishinan Ilimi, Ali Haruna Makoda, ta ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci a lamarin, kamar yadda wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatarsa, Bashir Baffa ta bayyana.
Shi ma Darekan Hukumar Kula da Makarantar Sakandire a Kano, Alhaji Abbas Abdullahi, ya bayyana damuwa kan lamarin, yana mai gargaɗin ɗalibai da su guji ɗaukar doka a hannunsu.