✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano za ta binciki musabbabin gobarar kasuwar Farm Center

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin da zai bincike musabbabin tashin gobarar da aka samu a kwanan nan a kasuwar wayoyin hannu ta Farm…

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin da zai binciki musabbabin gobarar da ta tashi a kwanan nan a kasuwar wayoyin hannu ta Farm Center da ke jihar.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai gobara ta tashi a kasuwar wacce aka yi kiyasin ta kone shaguna sama da 300 tare da janyo wa ’yan kasuwa asarar miliyoyin Naira.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Ibrahim ne ya rantsar da kwamitin a madadin Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Kwamitin dai kasance karkashin jagorancin Kwamishinan Ayyuka na Musammanna jihar, Alhaji Umar Ibrahim kuma yana da wakilai daga hukumomin gwamnati da jami’an tsaro da ma manyan masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci.

An dai dora wa kwamitin alhakin gano ainihin abin da ya haddasa gobarar sannan ya gano yawan asarar da aka tafka da kuma bayar da shawarwarin kauce wa sake aukurar irin ta a nan gaba.

Sakataren gwamnatin dai ya hori kwamitin da yin aiki tukuru wajen ganin ya sauke nauyin da aka dora masa.

Ya kuma yi kira ga kungiyoyi da daidaikun jama’a masu hannu da shuni da su taimaka wa ’yan kasuwar da tallafi ta hanyar asusun da gwamnati ta tanada, yana mai ba da tabbacin cewa za a yi adalci wajen rabon tallafin da aka tara.

Ana sa ran kwamitin zai kammala aikinsa tare da mika rahotonsa cikin mako daya daga kaddamar da shi.