Gobara ta tashi a Kwalejin Karatun Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci mallakin fitaccen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ke Rafin Albasa, a Jihar Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayan cikinta.
Binciken wakilinmu ya gano cewa gobarar ta lalata bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan kwamfuta, da ɗakunan karatu.
- Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa
- Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa
An kuma rasa kayan sawa na malamai da ɗalibai, katifu, barguna da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.
Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Sai dai daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce sun gode wa Allah da ba a rasa rai ko samun rauni ba.
“Lamarin ya faru ne bayan an kammala karatu da yamma, kuma muna godiya ga jami’an kashe gobara da suka kwashe sa’o’i suna ƙoƙarin kashe wutar,” in ji shi.
Ya ce makarantar na da alaƙa da Jami’ar Azhar da ke ƙasar Masar, kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo ne ya ƙaddamar da ita.
A cewarsa, makarantar kwana ce da ke bayar da ilimin boko da na Islamiyya tare da koyar da sana’o’i.
Kowace shekara ana yaye mahaddatan Alƙur’ani da dama a makarantar.
Ya ce an rasa litattafan Sheikh Dahiru Bauchi da na sauran malamai da dama, ciki har da kwamfutoci da kayan aikin makaranta.
Hukumar kashe gobara ta Jihar Bauchi ta bayyana cewa gobarar ta ƙone littattafai kusan 7,228, suturar ɗalibai kusan 583, gadaje 250, darduma mai faɗin mita 355, kujerun cin abinci 324, katifu, jakunkuna, kayan girki da sauran muhimman takardu da hotuna guda 150.
Ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.