✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a otal ɗin da ke ɗauke da Alhazan Najeriya 480 a Makkah

Rahotanni sun bayyana cewar ba a samu salwantar rayuka ba a yayin gobarar.

Gobara ta tashi a otal ɗin Imaratus Sanan da ke birnin Makkah a ƙasar Saudiyya, inda sama da alhazan Najeriya 48 suka sauka yayin aikin Hajjin shekarar 2025.

Otal ɗin yana unguwar Sharamansur a birnin Makkah.

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa dukkanin alhazan sun tsira kuma babu wanda ya ji rauni.

A cewar NAHCON, hukumomin gaggawa na Saudiyya da ma’aikatan otal ɗin sun gaggauta kashe wutar kafin ta bazu.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya ziyarci otal ɗin tare da wasu jami’an hukumar domin duba halin da ake ciki.

Ya bayar da umarnin a kwashe alhazan zuwa wani sabon otal cikin gaggawa, sannan ya yi alƙawarin tallafa musu.

“Muna gode wa Allah da babu rai da ya salwanta,” in ji shi.

Ya ce NAHCON za ta yi aiki da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa mahajjatan sun samu kulawa ta musamman.

“An riga an duba sabon wajen da za a sauke su, kuma an fara shirye-shiryen sauya wajen. NAHCON ta kuma yaba da saurin kai taimako da hukumomin Saudiyya da ma’aikatan otal ɗin suka yi.”

Wasu daga cikin mahajjatan sun shaida wa Aminiya cewa gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Asabar, a lokacin da mafi yawan su ke Mina wajen gudanar da jifar shaiɗan, ɗaya daga cikin manyan ayyukan aikin Hajji.

NAHCON ta ce za ta ci gaba da sanar da al’umma yayin da ake ciki da zarar ta samu sabbin bayanai.