✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa sunan Buhari

Tsohon shugaban ƙasar ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti a Landan bayan fama da jinya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno wadda aka fi sani da UNIMAID zuwa sunan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Wannan na zuwa na zuwa yayin taron majalisar zartarwa na musamman da aka gudanar tare da addu’o’i ga marigayi shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shugaba Bola Tinubu ne ya jagoranci taron wanda shugabannin majalisar tarayya da wasu daga cikin iyalan marigayin suka halarta.

Tsohon shugaban ƙasar ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti a Landan bayan fama da jinya.

An kuma binne shi ranar Talata a garin Daura na Jihar Katsina.